Tambaya :
Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa :
To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa :
a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.
Allah ne mafi sani.
Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406
©www.Darulfatawa.com
No comments:
Post a Comment