ArewaRulers

ShaFin ArewaRulers.com.ng ShaFine DaKe Kokarin Kawo MuKu Labaran Kannywood, Labaran Nishadi DaDai Sauransu .. KuCi Gaba Da Kasancewa Tare Damu

Social Media Widget

Thursday, 12 April 2018

Bani da ƙawa a Masana'antar kannywood - Inji Jaruma Umma Shehu

Shahararriyar jaruma wacce tauraronta ke kan haskawa a dandalin shirya fina-finan Hausa, Umma Shehu ta bayyana alakarta a farfajiyar Kannywood.

A cewar Umma bata da wata da ta rika a matsayin kawa a masana’antar saboda tana gujewa duk wani matsala ko abu da zai tunzura ta.

Jarumar ta jaddada cewa ita sana’arta kawai ta sanya a gaba saboda haka bata da lokacin kulla ko wace alaka ta kawance.

Idan dai bazaku manta ba a kwanakin baya ana ta ba’a ga jarumar bayan wani hira da tayi da Aminu Sheriff Momo a wani shirin talbijin sakamakon wani tambaya da ta kasa amsawa wanda ya shafi addini.

Jarumar ta kuma jaddada cewa ita batayi fushi ba akan abunda ya faru a tsakanin su.

No comments:

Post a Comment

Pages