Daga Habu Dan Sarki
Mai alfarma sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar na uku ya yi kira ga sauran Musulmi su rika nuna halayen kwarai a rayuwar su, wanda hakan zai sanya al'umma amincewa da su, kuma ya jawo hankalin wadanda ba Musulmi ba ga kyakkyawar tarbiyya da addinin Musulunci ke koyarwa.
Wannan na daga cikin sakon da Sarkin Musulmin ya aika wajen mika gudunmawar al'ummar Musulmi ga Malam Bashir Usman Idris mutumin da ya tsinci wasu makudan kudade har naira dubu 582 da dari 450 a cikin Keke Napep din da yake aikin haya da shi a Jos, wanda kuma ya mayar da kudaden ga matar da ta manta da kudade, Maman Ijima wacce 'yar kabilar Igbo ce dake harkar kasuwanci a kasuwar dare.
Da yake gabatar da sakon ga wannan bawan Allah, mai martaba Sarkin Wase wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Jama'atu Nasril Islam, Dr Muhammad Sambo Haruna, ya bayyana cewa an ba da wannan gudunmawa ne domin karfafawa Malam Bashir da sauran Musulmi gwiwa ga ayyukan alheri.
Ya ce, mai alfarma sarkin Musulmi da wasu mutane tara su ne suka hada kudi kimanin naira miliyan daya da dubu dari daya, don agazawa rayuwar sa, sakamakon halin kuncin rayuwa da yake fuskanta shi da iyalinsa.
Sakataren watsa labarai na kungiyar Jama'atu Nasril Islam a jihar Filato Alhaji Sani Mudi ya sanar da cewa, an yi amfani da kudaden wajen saya masa sabon Keke Napep da kudin sa ya haura naira dubu dari 6, da kuma firji na sayar da kayan sanyi da injin din markade, wanda aka bai wa matar Malam Bashir, Malama Hajara Dauda, saboda kokarin ta na karfafa masa gwiwa don ya mayar da kudaden.
Sannan an ba shi naira dubu 120 don biyan kudin makarantar yaransa da kudin hayar da ake bin sa bashi.
Bayan an mika masa sabon Keke Napep din dakamatsaya masa an kuma ba shi naira dubu 50 wacce zai yi amfani da ita wajen sayen lamba da yin rijista. Ita ma kuma matar sa an bata naira dubu 20 don ta ja jari a sana'ar da za ta yi.
Malam Bashir Usman wanda ya karbi kayan cikin hawaye, ya yi godiya ga mai alfarma sarkin Musulmi da daukacin wadanda suka taimaka masa, tare da kira ga abokan aikinsa da sauran Musulmi su zama masu halaye na kwarai, kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.
Malam Bashir Usman Idris na da aure da yara hudu.
©Zuma Times Hausa
No comments:
Post a Comment