Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bayyana cewa shi masoyin shugaban kasa Muhammadu Buharine na gani na fada kuma yana mishi biyayya sosai ta yanda koda zai umarceshi ya fada wuta babu wata-wata zai mishi biyayya.
Gwamna Bello ya bayyana hakane da yake bayar da amsa akan goyon bayan shugaba Buhari akan kin amincewa da karawa shuwagabannin jam'iyyar APC wa'adi inda ya bukaci a yi zabe dan samar da sabbin shuwagabannin.
Da yake amsa tambaya akan dalilin da yasa a farko ya goyi bayan a baiwa shuwagabannin APC din karin lokaci,
Gwamna Bello ya bayyana cewa yanzu ya goyi bayan a yi zabe kuma masu cewa yana da wata matsala da Tinubu ne shiyasa tun a farko ya goyi bayan karawa shuwagabannin APC wa'adi, ba gaskiya bane.
Tinubu shugaban shine shi kuwa shugaba Buhari shugaban kowane.
Dailypost.
No comments:
Post a Comment