Wadannan hotunan dan wasan kasar China ne da aka fi sani da Jet Li, wani masoyinshine ya dauki hotunan tare da Shi a Tibet inda suka hadu, mutumin ya saka hoton a dandalinshi na sada zumunta kuma hoton ya dauki hankulan mutane sosai inda masoyan jarumin suka rika nuna damuwa da irin halin da suka ganshi a ciki.
Jet Li ya taba tabbatar da cewa bashi da lafiya a shekarar 2013 amma yace ba abune wanda yayi tsanani ba, akwai kuma rashin lafiyar kasa tsayuwa na tsawon lokaci da Jet Li din yake fama da ita wadda ya samo dalilin ciwo da ya taba ji a kafa a yayin daukar wani fim.
Wasu da suka ga hoton sun rika kokwanton anya shine kuwa, ba hadawa akayiba?.
Saidai me magana da yawun Jet Li din ya bayyanawa Washington post cewa tabbas wannan hoton na Jet Li ne saidai yanayin daukar da akamai ce tasa mutane ke
ganinshi kamar ya galabaita sosai, ya kuma tabbatar da cewa Jet Lin bashi da lafiya amma ba wani abune da zai tayarda hankalin mutane ba.
No comments:
Post a Comment