Masana’antar Kannywood na da albarkattun kyawawa kuma kwararrun yan wasa mata da suka amsa sunansu na kyawawa.
Baya ga kyawu da wadannan mata ke da shi sun kasance masu kwazon aiki.
Munyi amfani da wannan dama wajen kawo maku kyawawan matan Kannywood da ke kasuwa har yanzu wato basu yi aure ba tukuna.
Rahama Sadau ta kasance matashiya wacce aka Haifa a ranar 7 ga watan Disamba, 1992 a jihar Kaduna. Tana da digiri a fannin kasuwanci. Tana daya daga cikin shahararrun yan matan Kaannywood, wacce ta shahara tun bayan bayyanarta a wani fim mai suna “Gani ga wane”. A kullun jarumar na mafarkin kasancewa shahararriya kuma mafarkinta ya zama gaskiya.
Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta kasance daya daga cikin matan Kannywood mafi kyau, tana da fuska mai matukar kyau da daukar hankali. An haifi Hadiza a ranar 1 ga watan Yuni 1989 a Libreville, a jumhuriyyar Gabon. Ta shaharane bayan ta fito a fim din Ă„li yaga Ali”.
Nafisa ta kasance daya daga cikin kwararrun jarumai da ked a kwazon aik. An haife ta a ranar 23 ga watan Janairu a garin Jos, Jihar Plateau. Nafisa ta kasance kyakyawa. Ta shahara a fim dinta na farko a 2010 wato “Sai wata rana.”
Fatima Washa ta kasance kyakyawar jaruma da ta fito a fina-nai da dama ciki harda Rariya. An haifi jarumar mai taushi Magana a ranar 21 ga watan Fabrairu 1993.
Hafsat Idris wacce aka fi sani da sunan wani fim da ta fito wato ‘Barauniya’ ta kasance daya daga cikin hadaddun matan kannywood. An haife ta a garin Shagamu amma yarasalin jihar Kano ce.
No comments:
Post a Comment