ArewaRulers

ShaFin ArewaRulers.com.ng ShaFine DaKe Kokarin Kawo MuKu Labaran Kannywood, Labaran Nishadi DaDai Sauransu .. KuCi Gaba Da Kasancewa Tare Damu

Social Media Widget

Sunday, 5 August 2018

Alamomi guda 10 da zaki gane mace 'yar madigo

Alamomi guda 10 da zaki gane mace 'yar madigo

A makon da ya gabata mun fara tabo batun bala’in da wasu mata ke jefa kansu a ciki ta dibi’ar madigo inda muka yi shimfida kan masifun da abin ke jawowa da kuma yadda ake bata wa iyaye yara ta hanyar jefa su a muguwar dabi’ar bayan sun ba su kyakkyawar tarbiyya. A wannan makon ma har yanzu dai muna kan maganar ta mata ‘yan madigo. Hakika duk wacce ta samu kanta cikin irin wannan jarabawa ta madigo to tana cikin fitinar rayuwa, ita kanta ba wai don tana jin dadin samun kanta a ciki ba ne, domin da yawansu sun san wannan abu ba abu ne me kyau ba ta kowacce fuska. Yana da kyau iyaye mu kula da rayuwar yaranmu mata don guje wa fadawa ire-iren wannan dabi’ar. A duk lokacin da uwa ta fahimci yarinyar ta tana da kawa da suke yawan ziyartar juna, to ta yi kokari ta yi bincike sosai. Ko ta gan ta da sabon wani abu da ta san ba ita ta saya mata ba ta binciket a inda ta samo, saboda wacce duk ke son rinjayar yarinyarta to tana iya mata kyauta ta bajinta. Alamomi Da Ake Gane Mace ‘Yar Madigo: Akwai alamomi masu tarin yawa wanda ake gani da ma wanda sai su kadai suke gane kansu. Kadan daga cikin wanda muke gani a zahiri sun hada da : 1. Suna da son yin kyauta ta bajinta ga mata musamman wadanda suka gani suna so. 2: Suna da mugun son yin dinkin riga matsattse me bayyana nononsu.

3: Idan sun hadu da wacce ta yi musu sun dinga yi ma ta farin ido wurin yi mata magana kenan don son jawo ra’ayinta. 4: Suna da son yabawa structure (kyan diri) na mace musamman wacce suke son jan ra’ayinta. 5: Sun fi koda kyau na mace fiye da namiji 6: Suna da mummunan kishi 7: Ba su damu da yin mu’amala da maza ba, kullum sun fi son su rabi mace cikin nuna sha’awa. 8: Suna da son kyalli da tsabta ta fitar hankali. 9: Suna da son yin mu’amala da kalolin turaruka. 10: Suna son saka sarka a kakarsu da zobe a yatsar kafar, duk da yanzu kusan an mayar da yin hakan gaye amma nasu na musamman ne.

Wadannan su ne kadan daga cikin alamomin da za a iya gane ‘yan madigo da su, amma ba su kenan ba. Kamar yadda na fadi a sama, akwai wasu alamomin da sai su da ke cikin muguwar dabi’ar ke iya ganewa ko kuma idan an yi la’akari da abubuwan da suke aikatawa da zarar sun hadu a tsakaninsu.

Iyaye sai mu kula a duk lokacin da muka ga wata alama makamanciyar wadannan ga yaranmu ko wacce ke mu’amala da yaranmu mata sai mu yi kokari mu yi wa tufkar hanci. A karshe wadanda suka samu kansu cikin wannan ibtila’i ta madigo muna yi musu addu’a da fatan nan gaba Ubangiji ya yaye musu ya raba su da ita, Allah ya shirya mu, ya tsare mu da sharrin mutanen zamanin namu, amin. . Copyright @Leadershipayau

No comments:

Post a Comment

Pages