A wata hira da tayi da manema wata DPO din 'yan sanda a Abuja ta bayyana yanda wasu 'yan daba suka wahalar da ita, yayin da suka je kama kayan sata a wata kasuwa dake Abuja. CSP Nana Bature Garba tace sai da aka gargade ta akan cewar kar ta sake ta shiga kasuwar Panteka dake unguwar Mpape a birnin Abuja, saboda irin hadarin da ke cikin kasuwar.
Ga dai irin bayanin da ta yiwa manema labarai. "Sunana CSP Nana Bature Garba. Ina so na bayyana muku labarin abinda ya faru dani lokacin da na ke DPO Mpape. Lokacin dana je Mpape suna da wata ka'ida cewa baka isa ka shiga kasuwar Panteka ka kama wani ba, ko ka dauki kayan mutane da aka sace a wajen.
Ni kuma sai nace ya za'ayi a ce 'yan sanda na wuri ace ba za'a shiga wurin ba, ni kam sai na shiga. Na tara 'yan sanda nace mu je. Ko kafin muje wurin ma mutanen Mpape suka dinga zuwa suna gargadina akan kada mu shiga wurin.
Abinda nake tunani shine, kamar akwai masu kai musu rahoto, domin kuwa ina kyautata zaton, kamar sun samu labarin muna zuwa. Domin kuwa muna zuwa wurin suka zagaye mu, suka sakar mana karnuka, muna budewa karnukan wuta, kamar daman abinda suke jira kenan, suka dinga jifan mu da duwatsu da sanduna ta ko ina a jikin mu.
A cikin 'yan sanda mu 18 da muka je wurin babu wanda bai ji ciwo ba. Sai da suka yi mana dukan tsiya, domin ko ni kaina da nake DPO sai da suka yaga min kayana suka yi mini tsirara, sai wata mata ce ta zo ta bani zani na daura. Sannan muka yi waya aka kawo mana agaji, kafin 'yan agajin su zo mun riga mun galabaita, ko tashi bama iya yi.
Da Allah ya bani lafiya, na ce ni kuwa wannan wurin ko menene a ciki sai na sani, na ce sai na sake komawa, saboda haka sai na rubutawa kwamishinana, na ce ina so a taimake ni mu samu a zo mu sake shiga wannan wurin, muga abinda za'a iya yi.
Sai ya ce to, tun daga wannan lokacin muka buda hanya, muke samu muna shiga wannan wuri, duk wanda aka yiwa sata zamu je wurin ayi bincike a kama wanda yake da laifi." Wannan shine takaitaccen labari na da gwagwarmayar dana sha a kasuwar Panteka dake Mpape Abuja.
No comments:
Post a Comment