'Yan sandan kasar Indiya sun cafke wata mace da ta yanke al'aurar mijinta tare da aran na kare da farkanta.
A cewar labarin da kafar AFP ta rawaito,a ranar 30 ga watan Yulin bana,a garin Vellore na yankin Tamil Nadu, wata mace mai suna Jayanthi mai shekaru 45 da haifuwa da mijinta, sun yanke shawarar zuwa gidan kallon wasan kwaikwayo,inda daga bisani ta sulale don ganawa da farkanta.
Bayan minti 30, sai maigidan ya dukufa neman ta.Can bayan wani lokaci sai ya yi kacibus da ita da farkanta a wani lambu.Nan take fada ya barke.
Yayin da ake fafata rikici tsakani mai gida da farka, wandon mijin Jayanthi ya fadi kasa.Abinda yasa ta yi hanzari ta saka baki ta guntsire al'aurarsa tare da aran na kare da farkanta.
Mutanen garin Nadu sun garzaya da mijin wanda jinin jikinsa ke ci gaba da malala,zuwa asibiti mafi kusa.
An cafke matar a ranar 1 ga watan Agustan da ya gabata,mijin kuma ana ci gaba da
jinyar sa a asibiti,inji helkwatar 'yan sanda.
A cewar jaridar The Times ta India,an garkame Jayanthi wacce ta karbi laifinta a kurkukun mata na Vellore.
TRThausa.
No comments:
Post a Comment