Duniyarnan sai mutum yayi tunanin ya gama jin abin mamaki sai wani sabo ya fito, wani labarine daya fito daga kasar China ke bayyana wasu ma'aurata da sukayi aure sama da shekaru 4 amma matar tana nan a sabuwar budurwarta saboda sunata yin jima'ai ba ta daidaiba a rashin sani, damuwar rashin haihuwa da suka shiga ciki ce ta sa labarin ya bayyana.
Ma'auratan wanda ba'a bayyana sunayensu ba saidai shekaru, matar tana da shekaru 24 mijin kuwa yana da shekaru 26, kamar yanda kafar watsa labarai ta Mirror ta kasar Ingila ta ruwaito.
Sunje asibiti sukawa likita korafin cewa suna ta jima'ai akai-akai tun bayan aurensu, yanzu shekaru 4 kenan amma babu maganar daukar ciki. Likitar da suka samu me suna Liu Hongmei ta bayyana cewa ma'auratan matasane kuma suna da lafiya dan haka abin da ban mamaki.
Matar ta mata korafin cewa tana jin zafi sosai lokacin jima'in amma saboda son haihuwa take jurewa.
Likita Liu ta bayyana cewa, ta sa a bincika matar sai suka gano wani abu me matukar ban mamaki, abinda suka gano kuwa shine matar haryanzu budurcinta na nan kamar budurwar da bata san namiji ba.
Da bincike yayi tsanani sai aka gano ashe ta dubura suke jima'ai shiyasa bata dauki ciki ba.
Bayan gano hakane, likita Liu ta zaunar da ma'auratan ta musu hudubar yanda ake jima'ai sannan ta basu littafin dake koya ilimin jima'i.
Da take hira da manema labarai, likitar tace, abin mamakine kuma ba'a cika samun irin wannan lamari ba ace ma'aurata sunyi aure tsawon shekara 4 amma basu san yanda ake daukar ciki ba.
Bayan 'yan watanni kadan sai ga ma'auratan sun dawo da kyautar kwai 100 da kaza ga asibitin saboda matar ta dauki ciki.
No comments:
Post a Comment