Wani wasan kwaikwayo ya auku a sananniyar
kasuwar Ogbeogonogo dake garin Asaba, cikin
jihar Delta a yayin da wani da ake zargin mahauci
ne ya yi mai matsakaicin shekara lokacin da ya yi
kokarin yiwa wata matar aure fyade a cikin
kasuwar. Lamarin ya auku ne a ranar asabara data gabata
kuma lamarin ya auku ne da misalign karfe biyu
na rana a lokacin da matar take kan sa’anar ta ta
sayar manja da kayan masarufi. Wata ganau mai suna Janet Agbou ta shedawa
kafar Daily Post cewar, mahaukacin mai suna
Simeon wanda yake sanye da yagaggun sitira ya
yi kokarin hawan bayan matar, inda hakan ya
janyo farfashewar kwalaben ta dake cike da
manja. Janet Agbou ta kara da cewar, mahaukacin ya
samu nasarar cire mata zani har ya samu danne ta
kuma ga dukkan alamu mutumin mahaukaci ne.
A cewar Janet Agbou mahaukacin ya yi kokarin
sanya alurar sa a cikin gaban matar, inda masu
wucewa suka kawo mata dauki suka kuma fara danawa mahaukacin na jaki. Daga baya an mika mahaukacin ga ‘yan sanda na
gundumar “A”, inda bayan da suka gudanar da
bincike suka gano cewar mahaukaci ne.
Da take
hira da kafar ta Daily Post matar wadda ta bukaci
kar a ambaci sunan ta tace lamarin ya girgizata. A cewar matar, “ Ji kawai na yi an kama ni ta
baya, kuma wanda ya kama ni din yana ta
kokarin keta mutuncina, wanda a kokowar da
muke yi ne sai muka fadi a kasa a tare, inda na
fara ihun a kawo mini dauki. Gungun mutane sun
bashi kashi daga baya aka mika shi ga ‘yan sanda. Ta kara da cewa, ni matar aure ce mai ‘yaya uku,
wannan aikin shedan ne kuma na godewa Allah
da ya tsyar da abin a nan domin ban taba sanin
wannan lamarin zai auku dani ba.
Da yake jawabi
akan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan
jihar DSP Aniamaka Andrew ya ce, duk da jibgar da mahaukacin yasha bai ce uffan ba. Ya sanar da cewar munyi amannar a bisa
binciken da muka gudanar mutumin mahaukaci
ne kuma baza mu iya tsare shi ba mun dai kashi
asibi don ayi masa magani.
No comments:
Post a Comment