- Masana’atar fina-finan Hausa ba za ta cigaba ba sai an daina fina-finan da basu da al-kibla inji Momoh Fitaccen dan wasan kwaikwayo na fina-finan Kannywood, Aminu Sherrif Momoh, yace masana’atar fina-finan Hausa ba za ta cigaba ba sai an daina fina-finan da basu da al-kibla.
Aminu Sherrif ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da BBC Hausa a jihar Kano.
Fitaccen jarumin yace babban kalubalaen da suke fuskanta itace manufa daya da zai kai masana’antar gaba da kuma bunkasa harshen Hausa. “Amma idan aka cigaba da yin fina-finan Hausa marasa al-kibla babu inda za a kai,” inji Momoh.
Momoh yace manufar sa na shiga masana’antar fim din Hausa, shine bunkasa harshe da al’adun Hausa a kasashen duniya.
No comments:
Post a Comment