Dailypost ta rawaito cewa an sallamo yaron shugaba Buhari, Yusuf Buhari daga asibitin Cedarcrest a yau bayan jinyar da ya yi sakamakon hatsarin babur a Abuja.
shugaba Buhari na musamman kan kafafin sada zumunta, Bashir Ahmad ya tabbatar da samun saukin Yusuf tare da sallamo shi daga asibitin Cedarcrest.
A ranar 26 ga watan Disamba ne aka kwantar da Yusuf Buhari biyo bayan hatsarin babur daya rutsa da shi a Abuja, bayan nan ne aka farfado da shi babban asibitin Cedarcrest inda aka yi masa tiyata, kuma a yanzu haka ya samu sauki sosai har an sallamo shi daga asibitin.
No comments:
Post a Comment