Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ta yafe wa fitacciyar jarumar fim Rahama Sadau dukkan laifukan da ta yi, wadanda suka janyo aka hana ta yin fim.
Shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakalla, ya shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa, "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".
Afakalla ya kara da cewa sun dauki wannan mataki ne bisa la'akari da gafarar da jarumar ta nemi a yi mata kwanakin baya.
A cewarsa, "Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta al'umar da take ciki.
"Don haka a matsayinmu na 'yan-Adam wadanda kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi", in ji shi.
A watan Oktoban da ya gabata ne shahararriyar jarumar ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.
A wata wasikar da ta aike wa kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa, MOPPAN, Rahama ta nemi afuwa a kan abin da ta yi, tana mai cewa "kuskure ne," kuma za ta "kiyaye gaba".
A wancan lokacin, Shugaban MOPPAN Kabiru Maikaba ya shaida wa BBC cewa kungiyar za ta sanar da matsayin da ta dauka a kan afuwar da jarumar ta nema bayan shugabanninta sun tattauna a hukumance.
Sai dai har yanzu kungiyar ba ta sanar da matakin da dauka ba.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa kan 'yan kungiyar ya rabu game da batun - inda wasu ke son a yafe mata yayin da wasu suka ki amincewa da hakan.
Da alama wannan ne ya sa fitaccen darakta Yaseen Auwal wanda ke goyon bayan jarumar ya nuna matukar bacin ransa game da kafar-ungulun da yake ganin wasu na yi ga batun.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, daraktan ya yaba wa shugaban hukumar tace fina-finan jihar Kano saboda kokarin da yake yi wurin ganin an dawo da ita fagen fim, sannan ya soki mutanen da ke kawo tsaiko cikin lamarin.
A cewarsa, "Allah Sarki bawan Allah Ismai'ila Na'abba, muna kara godiya bisa abin da ka yi a kan Rahama Sadau. Allah ya saka da alheri...ka yi naka mun gode; ka bar mu da ragowar...".
Rahama Sadau, wacce yanzu haka take kasar Cyprus inda take karatu, na shirin fitar da sabon fim dinta mai suna Dan Iya a wannan shekarar.
No comments:
Post a Comment