Daya daga cikin yaran marigayi Alhaji Mamman Shata, fitaccen mawaki kuma wanda ya raya kasar hausa da wakoki wato Hajiya Halima Mamman Shata ta bayyana anniyarta na fitowa takarar majalisar dokoki na jihar Katsina.
Hirar ta da jaridar RARIYA Hajiya Halima tana mai cewa ta gaji mahaifin ta a bangaren siyasa don haka zata daukaka wanan gado na fitowa takara domin wakiltar yankin Funtua a zaben 2019 dake nan tafe.
Ta bada dalilan daya sa zata fito takara kamar haka; "Na fito domin in bada guddumuwa ga cigaba karamar Hukumar Funtua da kawo kudurorin da za su kawo cigaban Matan da inganta rayuwar su a jihar Katsina da kasa baki daya.
"Mata suna da rawar da za su taka, a harkar siyasa amma mun yi barci an bar mu a baya musamman a arewacin Nijeriya, kalilan ne ke fitowa takara, saboda wadansu dalilai.
Kuma mu mata mune muka fi fitowa a ranar zabe, kuma kullum mune ake bari a baya. Idan Allah ya bani nasara zan tabbatar da an yi dokoki da za ta inganta rayuwar matan jihar Katsina da kuma karfafa rayuwar su".
Halima Shata ta kara da cewa "koda yaushe ina kara samun kwarin gwiwa a harkar siyasa saboda mahaifinmu dan siyasa ne, Amma ni na taso naga yana harkokin siyasa wadda har ya taba zama shugaban jam'iyyar da kuma takarar shugabanci kasar nan kuma cikin yayansa ina alfahari da na gaje shi bangaren siyasa, kuma zan cigaba da jajircewa domin ita ce matakin nasara.
Daga karshen yar gidan shaharen mawakin tayi ma Gwamna Aminu Bello Masari godiya bisa kokarin yake na bude kofofi ga mata don fitowa a dama dasu a harkar siyasa.
Daga: Pulse Nigeria
No comments:
Post a Comment