Matar tace bata da labarin cewa Jamil zaiyi aure kuma shima be gaya mata ba sai da cikinshi da take dauke dashi yakai watanni takwas, tace yanzu ta haifi jaririnta dan watanni biyu kuma yayi kama da Jamil din sosai. Tace ta bukaci Jamil din yazo ayi gwajin kwayoyin halitta dan a tabbatar da cewa danshine amma ya kiya.
Saidai wai ya biyata kudi ta tafi ta bar kasarnan da jaririn dan tayi renonshi a wata kasa can, matar 'yar shekaru 22 tace tunda ya nuna mata shi me kudine dan haka ta bukaci ya biyata miliyan dari.
Amma lauyanshi ya kiya, tace abinda jamil yace zai iya bata shine dubu arba'in duk wata ko kuma miliyan biyar daga nan karta kara nemanshi, amma tace ita taki amincewa da hakan domin miliyan biyar ko dubu arba'in duk wata babu abinda zatayi wajan kula da jaririn.
Tace ta gama hidimar daukar cikin bata yiwa Jamil maganaba dan haka bawai neman kudine yasa tace ya bata miliyan dari ba, tunda yace beson ganinta ko dan nashi to ita zata raini jaririn amma sai ya biyata kudin da tasan cewa asusun bankinta zai tumbatsa.
Ta kara da cewa yanzu lauya na biyu kenan dake kareta akan wannan lamari kuma suna mata barazana, idan bata amince da kudin da yace zai bata ba zasu kai kara kotu su kwace jaririn daga hannunta, harma sun shirya wani sako da aka aikawa matar jamil din na barazana sunce wai itace ta aikashi duk dan suyi maganinta kamar yanda sukace dan haka tace idan wani abu ya faru da ita ko jaririnta sune sila.
Kuma ta janye daga tattaunawar da suke zata tafi kotu tunda bai shirya biyanta abinda ta bukata ba.
No comments:
Post a Comment